Yadda Garuruwan Jos Ke Kokarin Hadin Kai Bayan Shekaru Cikin Rikici (1)


Tare da taimakon wata kungiya mai zaman kanta, al’ummar wasu garuruwa guda biyu da suka fada rikici a 2001 sun samu hanyar da za su zauna lafiya da juna. Wasu harare da mayar da martani da ya faru a tsakanin kiristocin unguwar Balkazai da kuma musulman unguwar Mai Damisa sun janyo asarar daruruwan rayuka da gidaje. Manyan da kungiyar ‘Youth Initiative Against Violence and Human Rights Abuse’ ta horar suna bawa matasa labaran zaman lafiya da ya wakana a Jos. Samarin da kungiyar ‘Jos Stakeholders for Peace’ ta horar kuma sun yarda su ajiye makamansu.

Related Stories