Rababben Birni (2): Addini Ya Raba Mazauna Jos, Kwallon Kafa Tana Hadasu


Tare da yan wasan kungiyoyin kwallon kafa na “Reconciliation” (Sulhu), “Peace” (zaman lafiya), “Love” (Soyayya), “Humanity” (Mutuntaka) da “Forgiveness” (Yafiya); wadanda kungiyar “Face of Peace Global” ta shirya, sun fara kokarin cire duk wani tsoro da rikicin addini ya dasa a garin a tsawon lokaci. Bayan shekaru 18 ana rikici tsakanin musulmi da kiristoci ta yadda har mutane suka koma zama a mabanbanta garuruwa, kocinan kungiyoyin kwallon kafa sun hada yan wasan da aka cakudasu ta fuskar addini da makotaka.

Related Stories